Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2021

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2021.

1563237
Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 14.01.2021

Yeni Safak: Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyan cewa, za su tabbatar da komai suna samar da shi a cikin kasar yadda ya kamata. A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi a wajen bayar da kyaututtukan Kungiyar Masu Gidajen Rediyo da Talabijin da aka gudanar a fadarsa ya ce, nan da wani dan lokaci In sha Allahu za a samar da manhajojin aika sakonni na cikin gida.

 

Sabah: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu bayan gudanar da taron Turkiyya-Azabaijan-Pakistan a birnin Islamabad ya gudanar da taron manema labarai inda ya ce, sun dauki kwararan matakan hadin kai a taron da suka gudanar. Ya ce "Mun dauki matakan hada kai a bangarorin tsaro, walwala da kwanciyar hankali".

 

Haber Turk: Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya baiwa Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bayanai game da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ta jagoranci Shugaban Azabaijan Ilham Aliyev da Firaministan Armeniya Nikol Pashinya suka sanya hannu a kai game da yankin Nagorno-Karabakh. Shugabannin biyu sun tattauna ta wayar tarho inda suka sake jadda kudirinsu na kara karfafa alakar Turkiyya da Rasha. Sun kuma yi duba kan cibiyoy,n Turkiyya-Rasha da za a kafa don sanya idanu wajen tabbatar da aiki da tsagaita wutar.

 

Star: Bayan amincewa da yin amfani da allurar riga-kafin Corona da Turkiyya ta saya daga China, an fara yi wa Ministan Lafiya na Kasar Fahrettin Koca allurar a Babban Asibitin Ankara. Koca ya ce,akwai bukatar a yi wa kowa riga-kafin Corona, saboda hanyar samun kariya mafi inganci daga cutar ita ce riga-kafi. Idan ana so a koma rayuwa yadda ya kamata to sai an yi riga-kafin.

 

Hurriyet: Ministan Masana'antu da Fasahar Kere-Kere na Turkiyya Mustafa Varank ya shaida cewa, kayan da Turkiyya ta samar a watan Nuwamban bara ya sanya ta zama daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya. Duk da matsalolin da aka fuskanta, samar da kaya a shekara ya karu da kaso 11 inda a kowanne wata kuma da kaso 1,3. Manufar Turkiyya ita ce wannan abu ya ci gaba a shekarar 2021.Labarai masu alaka