Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.01.2021

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.01.2021.

1558894
Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.01.2021

Star: Shugaba Erdogan ya yi magana a wani taron manema labarai tare da Firaministan Albaniya Edi Rama, wanda ke Ankara babban birnin kasar, bayan tattaunawar da suka yi da juna da wakilai. Erdogan ya bayyana cewar suna shirin kara saka hannun jari a aiyukan more rayuwa da yawon bude ido a Albaniya, kuma suna shirin daukar matakan hadin kan tattalin arziki da wannan kasar zuwa wani sabon matakan yaki da ta'addanci, kuma 'yan ta'addar FETO na cutar da dukkan kasashen 2. Hukumomin Turkiyya da suka hada da Asusun Ma'arif na tare da Turkiyya.


Haber Turk: A lokacin da masu zanga-zanga suka farwa ginin majalisar dokokin Amurka, Turkiyya ta fitar da sanarwa. Sanarwar Turkiyya ta yi kira ga dukkan bangarori da su daidaita al'amura da nutsuwa. Sanarwar ta ce "Muna da damuwa game da farwa ginin majalisar dokoki da masu zanga-zanga suka yi."

 

Hurriyet: Shugaban Kasar Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus Ersin Tatar ya yi kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres cewa, ya kamata su samar da tsari na adalci tsakanin bangarori 2 da ke Tsibirin.

 

Sabah: Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa na Turkiyya Fatih Donmez ya yi jawabi a wajen taron "Makamashin Rana" da Kungiyar Masu Samar da Makamashi daga Rana ta shirya. Donmez ya fadi cewa, samar da makamashi mai sabuntuwa ya habaka sosai a Turkiyya a lokacin da ake fama da cutar Corona. Makamashin da Turkiyya ke samarwa da ake sabunta shi ya kai megawatt dubu 49,550.

 

Vatan: A shekarar 2020 da ta gabata mutane dubu 242,787 ne suka ziyarci gidan adana kayan tarihi na gundumar Demre da ke Antalya inda aka samu kudi da suka kai yawan Lira miliyan 5,605,494.Labarai masu alaka