Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 30.06.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 30.06.2020.

1446073
Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 30.06.2020

Yenisafak "The Independent: Zargin da Faransa ke wa Turkiyya game da yanayin Libiya ya zama abu mai ban dariya"

A ra'ayoyin jama'a, sun yi shekaru da yawa suna goyon bayan Haftar wanda ba su san yadda za su ja da baya ba. Madadin amincewa da kurakurai, zai fi sauƙi a ce Turkiyya ita ce ƙasar da ke haifar da waɗannan matsalolin. Jaridar The Independent ta rawaito cewa "Jami'an Faransa a yanzu sun zama abun ban dariya yayin da suke kokarin kare manufofinsu na Libiya, suna zargin dukkan matsalolin kasar kan Turkiyya."

 

Star "Ministan Harkokin Waje na Hungary kan EU a Kudancin Cyprus"

Ministan Harkokin Waje na kasar Hungary, Peter Szijjarto a yayin ziyarar aiki a Kudancin Cyprus ya bayyana cewar kungiyar kasashen Tarayyar Turai (EU) na magana daban game da Turkiyya a gaban mutane amma suna magana daban a sirri, matsala mafi girma a allakar Turkiyya da EU shine munafincinsu kan Turkiyya.  

 

Vatan "Minista Albayrak: Tattalin arzikin Turkiyya na kara kwarin gwiwa"

Ministan Baitul Mali da Kudi, Berat Albayrak ya bayyana cewar tattalin arzikin Turkiyya na kara kwarin gwiwa. Alkalumman Tabbatarwar tattalin arziki, wanda ya karu daga 51.3 zuwa 61.7 daga watan Afrilu zuwa Mayu, yayin da a watan Yuni ya tashi zuwa kashi 73.5. Za mu ci gaba a shekarar 2020 tare da wannan aikin kuma zai kara bunkasa a shekara mai zuwa."

 

Sabah "Jirgin lantarki na cikin gida da na kasa suna kan titin jirage"

Ministan Masana'antu da Fasaha, Mustafa Varank ya bayyana cewar jiragen lantarki na cikin gida da na kasa za su kasance a kan titin jirage kuma za a fara gwaji. Ministan Sufuri da Kayayyakin More Rayuwa, Adil Karaismailoglu ya ce jiragen zasu kasance a kan hanyoyin a karshen wannan shekarar kuma za a fara jigilar fasinjoji nan ba da jimawa ba.

 

Hurriyet "Cibiyoyin dabaru na kasashe uku"

Ministan Sufuri da Kayayyakin More Rayuwa, Adil Karaismailoglu da yake bayyana cewar kasuwanci ta yanar gizo (e-commerce) na samun ci gaba a duniya tare da tsarin annobar, ya ce "Za mu kafa kasuwancin yanar gizo a Ingila, Jamus da Rasha. Manufarmu ita ce sanya kasuwancin namu cikin ɗaya daga manyan 'yan wasa 5 a yankin."Labarai masu alaka