Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 21.05.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 21.05.2020.

1420992
Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 21.05.2020

Sabah: "Cavusoglu ya tattauna da takwaransa na Rasha Lavrov"
Ministan Harkokin Waje na Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov ta wayar tarho. Dangane da bayanai daga majiyoyin diflomasiyya, sun tattauna batun sabon nau'in cutar corona (Covid-19), yawon shakatawa da batutuwan yanki.

 

Hurriyet: "Minista Akar yayi bayanin: An kassara 'yan ta'adda 1411"
Ministan Tsaro na kasar Turkiyya, Hulusi Akar ya bayyana cewar ana ci gaba da magance ta'addanci a arewacin Siriya da Iraki kuma an kassara 'yan ta'adda 1411 tun daga ranar 1 ga watan Janairu.

 

Haber Turk: "Martani daga kakakin shugaban kasa game da shirin mamayewa na Isra'ila"
Kakakin Shugaban Kasa, İbrahim Kalin ya mayar da martani ga shirin Isra'ila game da mamayewa. Kalin ya bayyana cewar "Mun yi watsi da matakin Isra'ila na shirin Gabar Tekun Yamma, kuma muna kira ga duniya da ta dauki mataki. Turkiyya za ta ba da goyon baya kan dukkan matakan kauda manufofin mamamaye filayen Falasdinawa."

 

Star: "Bayani daga Minista Koca"
Ministan Lafiya na Turkiyya, Fahrettin Koca ya ce bayyana cewar al'ummarsu sun amince da matakan da aka dauka kan sabon nau'in cutar corona (Covid-19). Ministan Koca ya bayyana a cikin sanarwar ga manema labarai bayan taron Kwamitin Kimiyya a jiya cewar yaki da corona zai zama mafi girma da aka samu a cikin kwanakin nan. Matukar adadin sabbin mutane da suka kamu da cutar ya fadi kasa da dubu, toh faduwar nan zata zama babbar nasara." 

 

Vatan: "Sanarwar kididdigar amincewar mabukata na watan Mayu"
Cibiyar Kididdiga ta Turkiyya (TSI) ta ba da sanarwar amincewar mabukata na watan Mayu. Kiddigar amincewar mabukata ya ƙaru da kashi 8.5 cikin 100 a watan Mayu idan aka kwatanta da watan da ya gabata; kididdigar wacce ta kasance 54.9 a watan Afrilu, ta zama 59.5 a watan Mayu.Labarai masu alaka