Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.03.2020

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.03.2020.

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.03.2020

Yeni Safak: "Kasashe 69 na duniya sun nemi taimakon Turkiyya, mun aika taimako zuwa kasashe 17"

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi jawabi ga al'umar kasar game da matakan cutar coronavirus. Erdogan ya bayyana cewar "kawai buƙatarmu ga 'yan ƙasa shi ne su bi ka'idojin gargaɗi gaba ɗaya don hana yaduwar cutar a cikin kwanaki masu zuwa. Domin mu iya komawa rayuwarmu ta yau da kullun da wuri-wuri. Rayuwar kowanne ɗan ƙasa na da mahimmanci a gare mu. Muna kira don a zauna a gida a Turkiyya. A yau kasashe 69 na duniya bukaci taimako daga Turkiyya, an aika da taimako na gwargwadon iko zuwa kasashe 17."

 

Vatan: "Minista Koca ya sanar da adadin wadanda aka kwantar da"

Ministan Lafiya na Turkiyya, Fahrettin Koca ya yi magana game da adadin wadanda suka warke daga cutar coronavirus a Turkiyya inda ya bayyana cewar "Wani mara lafiya mai shekaru 65 da haihuwa, ya kasance cikin kula na kwanaki 8, ranar Talata aka sallame shi daga asibiti. An sallami wani kuma mai shekaru 60 ranar Laraba. Ya zuwa yanzu marasa lafiya 26 ne suka warke a Turkiyya. 

 

Sabah: "Minista Albayrak: Za mu fara da dukkanin kamfanoninmu"

Ministan Baitul Mali da Kudi na Turkiyya, Berat Albayrak a cikin sakon da ya yada game da matakan cutar coronavirus ta shafukansa na sada zumunta ya bayyana cewar, "A cikin iyaka na "Kare Garkuwar Tattalin Arziki", bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi zasu fara da "Tallafin Ci Gaban Aiki" ga dukkanin bangarorinmu da duk kamfanoninmu.

 

Hurriyet: "Jirgin ruwan kaya na Turkiyya na isar da kayayyakin kiwon lafiya zuwa Turkiyya"

A cikin tasirin gwagwarmayar duniya a wannan mawuyacin lokaci (barkewar cutar coronavirus), Jirgin ruwan kaya na Turkiyya na ci gaba da aikinsa na kawo magunguna da kayan aikin likita da ake bukata daga ko'ina cikin duniya zuwa Turkiyya. A wannan fanni, jirgin ruwan kaya na Turkiyya ya kawo kayan gwaje-gwaje masu sauri wadanda zasu iya gano kwayar cutar a cikin mintuna 15 da aka samu daga China zuwa Turkiyya.

 

Star: "An fara gwajin magunguna Amurka"

An fara amfani da magani wanda zai iya yin tasiri ga ƙwayar cutar ta coronavirus a cikin jihar New York ta Amurka.Labarai masu alaka