Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.05.2021

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.05.2021.

1634994
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.05.2021

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa daliban Afaka da aka yi garkuwa da sun isa helikwatar ‘yan sanda da ke jihar Kaduna.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da Naira biliyan 6.2 don aiwatar da aiyukan wutar lantarki a kasar.

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 165,273 cutar corona ta kama a kasar.

 

zdf.de: Kunshin Euro biliyan 2 da aka shirya don tallafawa ɗaliban da suka rage a ajinsu saboda matakan corona a Jamus ya sami karɓuwa daga Majalisar Ministoci.

Süddeutsche Zeitung: Shafin sada zumunta na Facebook ya yanke shawarar ci gaba da haramta asusun sada zumunta na Donald Trump, tsohon Shugaban Amurka.

Welt.de: Kashi ɗaya cikin huɗu na ‘yan Tarayyar Turai (EU) sun sami kashi na farko na allurar riga-kafi.

 

Le Monda: Matar da mijinta mai laifi ya kona ta da rai ta mutu a tsakiyar titi a birnin Merignac na Faransa.

France 24: Shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya gabatar da bayani kan bukin cika shekaru 200 da mutuwar Napoleon (sojan Faransa kuma dan siyasa), ya ce "Napoleon wani bangare ne na mu."

Le Parisien: An harbe wani dan sanda a birnin Avignon na Faransa lokacin da yake aikin kama masu sayar da miyagun kwayoyi.

 

Al-Quds Al-Arabi: Tarayyar Turai na neman Isra’ila mai mamaya da ta daina fadada matsugunanta.

Al-Quds Al-Arabi: Libiya .. Wata tawaga daga yankin Gabas ta ziyarci Tarabulus, babban birnin kasar tare da neman Firaministan Libiya Abdulhamid Dibeybe da ya hanzarta ziyarar Benghazi.

Al Jazeera: Majiyoyin diflomasiyya: "Babban gibin da ke tsakanin Tehran da Amurka ya dakatar da ci gaban tattaunawar ta Vienna."

 

El Pais: (Spaniya) Biyo bayan gazawar jam’iyyun ra’ayin rikau a farkon zaben Majalisar Dokoki na cikin gida da aka gudanar karkashin gwamnatin Madrid mai cin gashin kanta a ranar Talata (4 ga Mayu), wasu ‘yan majalisar daga Jam’iyyar PSOE ta Spaniya sun sanar da cewa sun yi imanin cewa farfadowar tattalin arzikin zai sauya lamarin.

El Mundo: (Spaniya) An yi hasashen cewa Ministan Kwadago, Yolanda Díaz zai zama sabon shugaban jam'iyyar bayan da shugaban Jam'iyyar Podemos, Pablo Iglesias ya fice daga siyasa.

TeleSur: (Venezuela) Abubuwan da suka faru tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a Kolombiya, wasu masu zanga-zanga biyu sun mutu a garin Pereira.

 

Lenta.ru: Yukren ta zargi Rasha da yin amfani da dandalin Majalisar Dinkin Duniya ba daidai ba.

TASS: An zaɓi mafi kyawun allurar riga-kafin sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19) a taron Majalisar Dinkin Duniya. An dauki Moderna a matsayin allurar riga-kafi mafi kyau.

Gazeta.ru: Masana a Amurka suna tunanin akwai yiwuwar cewa Shugaban Amurka Joe Biden da Shugaban Rasha Vladimir Putin za su tattauna a manyan biranen Czech Republic, Iceland, Slovenia ko Azabaijan.Labarai masu alaka