Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.04.2021

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.04.2021.

1615580
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 06.04.2021

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa Saudiyya ta bayyana ba da izinin aikin Hajji a Makkah ga mahajjatan da suka yi allurar riga-kafin Covid-19 kawai.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce Shugaba Buhari ya la’anci hare-haren ta’addanci da aka kai Helkwatar Rundunar ‘Yan Sanda da gidan yari a Owerri da ke jihar Imo.

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 163,330 cutar corona ta kama a kasar.

 

al-Düstur (Jaridar Jordan): Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun gudanar da bukin Talmudi a Masallacin al-Aqsa, wanda suka shiga karkashin kariyar 'yan sandan Isra'ila.

al-Quds al-Arabi: Tunisiya ta yi kira ga Turai da ta magance matsalar ‘yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

al-Raye al-Qatariyye (Jaridar Katar): Katar da Yukren sun karfafa hadin gwiwa tare da yarjejeniyoyi 2 da kuma yarjejeniyoyi guda 7 na fahimta.

 

Bild.de: Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya sanya hannu kan dokar da za ta ci gaba da rike shi kan karagar mulki har zuwa shekarar 2036.

Deutsche Welle: An daina sanya abun rufe fuska a Gibraltar. Yankin Gibraltar ya yi nasarar yin wa kowa allurar riga-kafin Covid-19. Kowa ya samu riga-kafi daga cutar.

ard.de: Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa (a cikin matakan yaki da Covid-19) ya kamata ‘yan Birtaniya su ɗan sami haƙuri don tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

 

La Vanguardia (Spaniya): A cikin Spaniya, ci gaba da yin allurar riga-kafi kan Covid-19 bai hana isowar barkewar cutar a karo na 4 ba.

El País (Spaniya): Covid-19: Kashi 10 na waɗanda suka kamu da cutar suna ci gaba da nuna alamun cutar watanni bayan warkewa.

Infobae (Ajantina): A ranakun farko na watan Afrilu, Uruguay da ke Kudancin Amurka, ta zama ƙasar da ta fi amfani da alluran riga-kafin Covid-19 ga kowane mutum a duniya.

 

Le Parisien: Ministan Tattalin Arzikin Faransa, Bruno Le Maire ya sanar da samar da sabon tallafi na Euro biliyan 4 ga kamfanin Air France.

Le Figaro: Covid-19: Ana sake buɗe wuraren adana kayan tarihi da filaye a Portugal, kuma an shirya sake buɗe shaguna a Landan, babban birnin Ingila.

France 24: Covid-19: Faransa za ta fara samar da allurar riga-kafi a kan iyakarta.

 

Gazeta.ru: Ma'aikatar Gwamnatin Amurka ta nemi Rasha da ta yi bayanin aikin sojojinta a kan iyaka da Yukren.

RIA informing: Shugaban Yukren, Vladimir Zelensky zai gana da Shugaba Recep Tayyip Erdogan kuma ya nemi da a aika da wata jigilar jiragen Bayraktar TB2 mara matuka zuwa Yukren yayin da halin da ake ciki a Donbass ke kara ta’azzara.

RBK: Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya sanya hannu kan kwaskwarimar da zai ba shi damar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.Labarai masu alaka