Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 01.04.2021

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 01.04.2021.

1612661
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 01.04.2021

Daily Trust: Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya na cewa jirgin saman yaki na soji da aka tura don yaki da ‘yan Boko Haram ya bace a Borno.

Daily Nigerian: Jaridar Daily Nigerian da ake bugawa a yanar gizo a Najeriya ta ce Gwamnatin Najeriya ta amince da dala miliyan 26 don aiyukan wutar lantarki a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Vanguard: Jaridar Vanguard da ake bugawa a Najeriya na cewa ya zuwa yanzu mutane 162,891 cutar corona ta kama a kasar.

 

Elquds Alarabi: Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yaba sasantawar Oman a Yemen tare da jaddada bukatar kawo karshen rikicin.

Aljazeera: Ministocin harkokin waje na kasashen Turai 18 sun yi alkawarin cewa za a hukunta "laifukan yaki" a Siriya.

Elraya: Katar ta kushe tashin hankali kan fararen hula a Siriya.

 

Deutsche Welle: Kasuwancin duniya yana murmurewa cikin sauri fiye da yada ake tsammani.

Der Spiegel: An karbe ikon lauyoyi 18 yayin wa'adin dokar karshe a Jamus.

Tagesschau: Kasashen EU sun kasa cimma burin allurar riga-kafi.

 

Le Figaro: Covid-19: (Shugaban Faransa) Emmanuel Macron ya yarda da "yin kuskure" a cikin yaki da annobar.

Le Monde: (Minista mai wakiltar ‘yan kasa) Marlène Schiappa ta tabbatar a Majalisar Dattawa cewa za a maye gurbin Observatory of Secularism da wani tsari daban.

 

El País (Spaniya): EU ta kasa cimma dukkan burukan allurar riga-kafi na kwatan farko.

Infobae (Ajantina): Rikicin soja a Brazil: (Shugaban Brazil) Jair Bolsonaro ya nada sabbin kwamandoji a Rundunar Sojojin kasar.

La Tercera (Chile): Rashin nasarar Masana'antar Baltimore ta Amurka ya haifar da asarar alluran riga-kafin Covid-19 kimanin miliyan 15 na Kamfanin Johnson & Johnson. 

 

RIA Novosti: Josep Borrell, Babban Wakilin Tarayyar Turai kan Harkokin Kasashen Waje da Manufofin Tsaro, ya bayyana shawarar da Moscow ta dauka na tura jami'an diflomasiyyar Turai 3 da suka halarci zanga-zangar (wacce aka yi a watan da ya gabata) daga kasar a matsayin "hari".

Gazeta.ru: Wakilin Hukumar Kula da Kare Hakkin Masu Sayan Kayayyaki da Lafiyar Dan Adam (Rospotrebnadzor) ya bayyana cewar annobar corona a Rasha na iya ƙarewa a watan Agusta.

Kommersant: Amurka ta tattauna da Rasha game da matakin soja kan iyakar Yukren.

 Labarai masu alaka