Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 20.01.2021
Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 20.01.2021.

n-tv: A yayin taron da gwamnatin tarayyar Jamus da na jihohi suka yi, an dauki matakin ci gaba da hana mutane zirga-zirga har nan da 14 ga Fabrairu. An kuma kara jaddada wajabcin saka takunkumi.
Seddeutsche Zeitung: Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ya sake saukar da hasashen habakar tattalin arziki na Jamus.
Frankfurter Algemeine Zeitung: Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo na zargin China da aikata kisan kare dangi ga jama'ar Uyghur.
Aljazeera: A jawabin bankwana da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi ya bayyana cewar, shi ne Shugaban Amurka na farko da bai yi yaki ba.
Al-qudus Al-Arabi: A ranar 20 ga Janairu din nan Joe Biden ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayi. Shugaban Kasar Amurka.
Aldostur: Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, gina matsugunai a yankunan Falasdinawa take dokokin kasa da kasa ne karara.
El Pais: Nan da watan Maris a Spaniya za a yiwa 'yan sama da shekaru 70 su miliyan 6 allurar riga-kafin cutar Corona.
Infobae: Rasha ta bayyana cewar allurar EpiVacCorona na yin riga-kafin Corona dari bisa dari.
Prensa Latina: Kashin farko na alluran riga-kafin Pfizer-BioNTech sun isa Panama.
Le Monde: Birnin Paris ne a kan gaba a Turai wajen mutuwar mutane sakamakon munanar yanayi da ababan hawa ke janyowa.
Le Matin: Cutar Corona ta janyo mutuwar mutum 1 daga cikin mutane 1000 a Swizalan.
Le Parisien: An gano cewar zango na 2 na yaduwar Corona ya fi kashe mutane da yawa.
TASS: Mutumin da ake sa ran zai zama Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana cewa, ba za a taba amincewa da Turkiyya ta mallaki S-400 kirar Rasha ba.
Jakadan Rasha a Amurka ya bayyana cewar, takunkumin da Amurka ta sakawa aikin Nord Stream-2 hamayya ce mara tushe kuma zai sanya dole Turai ta dinga sayen danyen man Amurka.
Lenta.ru: Wanda ake sa ran zai zama Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana cewar manufofin Rasha na Kasashen Waje sun ci karo da bukatun Amurka.