Manyan labaran wasu kasashen waje 14.01.2021

Manyan labaran wasu kasashen waje 14.01.2021

1563313
Manyan labaran wasu kasashen waje 14.01.2021

Daily Trust: Jihohin Zamfara, Imo da Rivers ba su ci jarrabawar gwamnatin Tarayya kan tsantseni da gaskiyar sarrafa kudade ba.

Daily Nigerian: An fara sayar da tikitin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta yanar gizo.

Leadership: Gwamnonin Arewacin Najeriya sun yi gargadi kan yada jita-jita game da riga-kafin cutar Corona.
 

Le Monde: An fara bincikar Ministan Shari’a na Faransa bisa zarginsa da amfani da mukaminsa ta mummunar hanya.

Le Monde: Kotun Paris ta yanke hukuncin ma tsanani ga wasu ‘yan sanda 3 bisa nuna wariya da cin zali da suka yi.

Le Soir: An samu rikici a Brussels Babban Birnin Beljiyom bayan kama wani matashi dan Afirka da aka yi.
 

Deutsche Welle: Hukumar Kula da Magunguna ta Turkiyya ta amince da a yi allurar riga-kafin Corona ta China bayan gwajin da aka kammala. Bayan amincewar, an fara yi wa Ministan Lafiya na kasar allurar.

DiePress.com: Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO ta ce, an gano sabon nau'in cutar Corona mafi saurin yaduwa a kasashen duniya 50.

Tagesschau.de: Ministan Lafiya na Jamus Jens Spahn ya ce, akwai bukatar matakan yaki da Corona su ci gaba har nan da watan Fabrairu.

 

Al-Dustour: Mutane 57 sun mutu sakamakon harin da Isra’ila ta kai Siriya.

Al-Qudus Al-Arabi: Shugaban Amurka Donald Trump ya zama shugaba na farko a tarihin kasar da sau 2 aka kai shi gaban majalisar dattawa don tsigewa.

Aljazeera: A karon farko an nada wani dan asalin kasar Siriya a matsayin Ministan Sufuri na Kanada.

 

Interfax: Dan adawar Rasha Aleksey Navalniy ya kasance a jerin sunayen wadanda 'Yan sandan Rasha suke nema tun watan Disamba.

RBK: Kwararrun bankin "Bank of America" da ke Amurka sun ce, kasuwanni a Rasha za su iya daidaita saboda nasarar da Joe Biden ya yi na zama Shugaban Kasa.

Lenta.ru: Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar da umarnin a fara yin allurar riga-kafi a fadin kasar daga mako mai zuwa.

 

El Pais: A Spaniya gwamnati ta yi alkawarin taimakawa wadanda dusar kankara ta illata.

TeleSur: Shafin Twitter na karamin ofishin jakadancin Mekziko da ke Dallas an bayyana cewar, daga 2008 zuwa 2018 an kashe 'yan Latin Amurka da ke rayuwa a Amurka (Hispanik) su dubu 19,998 ta hanyar harbi.Labarai masu alaka