Yau ce Ranar Zaman Lafiya ta Duniya

Ana gudanar da bukin tunawa da ranar da Jamus ta aiyana yaki akan Poland a matsayin "Ranar Zaman Lafiya ta Duniya" a kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma Türkiye.

1882367
Yau ce Ranar Zaman Lafiya ta Duniya

Ana gudanar da bukin tunawa da ranar da Jamus ta aiyana yaki akan Poland a matsayin "Ranar Zaman Lafiya ta Duniya" a kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma Türkiye. Bayan Yakin Duniya na biyu aka kafa Majalisar Dinkin Duniya don hana afkuwar wani yaki da barkewar yake-yake gaba daya. Duk da haka, an fuskanci rikice-rikice da yake-yake daga lokaci zuwa lokaci.

Lokacin da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya, kasashe mambobi 5 ne suka kafa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ba tare da ka'idar daidaito ba. Duk da cewa kasashe da dama sun soki wannan lamarin, wakilai 5 na dindindin na Kwamitin Tsaro na ci gaba da aiki har zuwa yau. Kamar yadda yake a batun Falasdinu, ba za a iya yanke shawarar hadin gwiwa ba, ba tare da daya daga cikin wadannan mambobi 5 ba.

Kalaman Shugaban kasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan da ke cewa “duniya ta fi kasashe 5”, wanda ya bayyana da karfi, na samun karuwar goyon baya a 'yan shekarun nan. Fatanmu shi ne Majalisar Dinkin Duniya, wacce ke da matukar muhimmanci wajen kiyaye zaman lafiya a duniya, ta yi hidima ga zaman lafiyar duniya baki daya tare da tsarin daidaito da rashin son kai.

Muna muku Barka da Ranar Zaman Lafiya ta Duniya a yau ranar 21 ga watan Satumba.Labarai masu alaka