Kashi 90 cikin darin kasashen Afirka ba zasu iya yiwa al’ummansu riga-kafin Korona ba

Kashi 90 cikin darin kasashen Afirka ba zasu yiwa kaso 10 cikin darin al'ummansu allurar riga-kafin Korona kafin watan Satumba ba

1657036
Kashi 90 cikin darin kasashen Afirka ba zasu iya yiwa al’ummansu riga-kafin Korona ba

Kashi 90 cikin darin kasashen Afirka ba zasu yiwa kaso 10 cikin darin al'ummansu allurar riga-kafin Korona kafin watan Satumba ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa hakan zai iya yiwuwa ne ıdan kasashen Afırka sun samu alluran riga-kafin Korona kwara miliyan 225.

A wani taron tattaunawa da manema labarai, daraktan Ofishin Yankin Afirka na Hukumar Lafiya ta Duniya Matshidiso Moeti, ya ce ba tare da wani muhimmin ci gaba ba game da samar da alluran rigakafin ba, kasashen Afirka bakwai ne za su cimma wannan buri.

A cikin allurai miliyan 32, Afirka tana da ƙasa da kaso daya cikin dari  na sama da alluran biliyan 2.1 na COVID-19 da ake gudanarwa a duniya.

Kashi cikin darin kusan mutane biliyan 1.3 na nahiyar sun karbi kashi daya kuma 'yan Afirka miliyan 9.4 ne ke da cikakkiyar rigakafin, in ji alkaluman WHO.Labarai masu alaka