Shugaba Erdogan ya ziyarci Brussels don halartar taron kolin NATO

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Brussels don halartar taron kolin kungiyar NATO

1657102
Shugaba Erdogan ya ziyarci Brussels don halartar taron kolin NATO

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Brussels don halartar taron kolin kungiyar NATO.

Shugaba Erdogan ya samu tarbo a filin tashi da saukar jiragen saman Melsbroek dake Brussels daga wakilin Turkiyya a NATO Basat Ozturk wakilin Turkiyya  a Tarayyar Turai Mehmet Kemal Bozay, Jakadan Turkiyya a Brussels Hasan Ulusoy, Shugaban Tawagar Sojojin Turkiyya Manjo Janar Ismail Uner, Babban Jami'in Ofishin Jakadancin Turkiyya a Brussels Umut Deniz da sauran jami'ai.

Shugaba Erdogan zai gana da shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO, Shugaban Amurka Joe Biden, Shugaban Lithuania Gitanas Nauseda, Shugaban Latvia Egils Levits, firaiministan Jamus Angela Merkel, firaiministan Birtaniya Boris Johnson da firaiministan Girka Kiryakos Mitsotakis.

Haka kuma an shirya Erdogan zai gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaiministan Holland Mark Rutte.

Baya ga kawancen da ke cikin kungiyar ta NATO, ana sa ran alakar kasashen biyu da batutuwan yankin za su kasance kan gaba a yayin tattaunawar.

Taron Erdogan da Biden zai zama ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu bayan zaben Biden a matsayin shugaban Amurka.

Babban ajandar wakilan Turkiyya da shugaba Erdogan ya jagoranta a taron NATO zai kasance girmamawa da samar da tsaro a yankinta. A wurin taron za a jaddada kudurin Turkiyya kan wadannan batutuwan.

Za a jaddada cewa Turkiyya kasa ce memba da ke cika ayyukanta daidai gwargwadon kawancen, kuma za a maimaita tayin hadin gwiwa a yaki da ta'addanci da kuma shiga tsakani a cikin rikice-rikicen da ake fama dashi.Labarai masu alaka