Mutane 13 sun rasa rayukansu a harin kungiyar PKK a Afrin

A harin da kungiyar ta'addar a ware ta YPG / PKK ta kai a yankin Afrin na Siriya, fararen hula 13 da aka ke samun kula a wani asibiti mai zaman kansa sun rasa rayukansu.

1656798

A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga Ofishin Hakimin Hatay, an bayyana cewa makami mai linzami samfurin Grad da kuma bindigogin igwa da kungiyar ta'adda ta YPG / PKK suka harba daga yankin Tel Rifat da ke karkashin gwamnatin Assad ya fada kan Bangaren Bayar da Agajin Gaggawa na wani asibiti mai zaman kansa da ke Afrin. 

An kuma bayyana cewa "Fararen hula 13 da ke samun kulawa a asibitin sun rasa rayukansu sannan wasu fararen hula 27 kuma sun jikkata." Labarai masu alaka