An tsare bakin haure 1000 a Libiya

An sanar da kame bakin haure 1000 a cikin kwanaki biyu kachal a kasar Libiya

1656972
An tsare bakin haure 1000 a Libiya

An sanar da kame bakin haure 1000 a cikin kwanaki biyu kachal a kasar Libiya.

Kamar yadda mai magana da yawun Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Safa Msehli ya yada a shafinsa ta twitter " A yankin mashigar Libiya a cikin kwanaki biyu kachal an kame bakin haure har guda 1000"

Ba'a dai bayar da cikekken bayanai game da lamarin ba.

Libiya ta kasance gabar da bakin haure dake neman haurawa zuwa Turai ke bi don cimma burinsu a cikin 'yan kwanakin nan.

 Labarai masu alaka