Wasu abubuwa sun fashe a wata masana'anta a Indiya

Mutane 4 ne suka rasa rayukansu, wasu 20 kuma suka samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a wata masana'antar samar da magunguna a jihar Tamil Nadu dake kudancin Indiya.

1639026

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce, a rukunin masana'antu na SIPCOT dake Tamil Nadu ne fashewar ta afku da safiyar Alhamis din nan.

Ma'aikatan masana'antar 4 sun rasa rayukansu, an kai wasu 20 da suka jikkata zuwa asibitin Cuddalore.

An fara gudanar da bincike game da ibtila'in.

 Labarai masu alaka