‘Yan sandan Isra’ila sun tsare Falasdinawa 13 a samamen da suka kai Gabashin Kudus

‘Yan sandan Isra’ila sun tsare Falasdinawa 13 a yankuna daban-daban na gabashin Kudus da ta mamaye

1636498
‘Yan sandan Isra’ila sun tsare Falasdinawa 13 a samamen da suka kai Gabashin Kudus

‘Yan sandan Isra’ila sun tsare Falasdinawa 13 a yankuna daban-daban na gabashin Kudus da ta mamaye.

A cikin labaran da hukumar Falasdinawa ta WAFA ta wallafa, an bayyana cewa, 'yan sandan Isra'ila sun kai samame a gidaje da dama a sassa daban-daban na Gabashin Kudus, musamman a tsohon gari inda Masjid al-Aqsa yake.

Rahoton wanda aka kafa bisa shaidun gani da ido, ya bayyana cewa Falasdinawa 13 ne ‘yan sandan Isra’ila suka tsare a yayin samamen.

Har yanzu babu wani bayani da ‘yan sandan Isra’ila suka yi game da tsarewar.Labarai masu alaka