Antonio Guterres ya nemi a sake zabensa a matsayin sakataren MDD

Antonio Guterres, wanda ya bayyana sake tsawaya takarar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ya yi alkawarin zama "mai shiga tsakani bisa gaskiya" kuma zai taka rawar "Maginin Gada" wajen warware rikice-rikicen da ke addabar duniya

1636504
Antonio Guterres ya nemi a sake zabensa a matsayin sakataren MDD

Antonio Guterres, wanda ya bayyana sake tsawaya takarar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ya yi alkawarin zama "mai shiga tsakani bisa gaskiya" kuma zai taka rawar "Maginin Gada" wajen warware rikice-rikicen da ke addabar duniya.

Baya ga Guterres, akwai wasu mutane 7 da ke yunkurin samun mukamin na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin da kasarsa ta Portugal ta zabi Guterres don wannan mukamin, sunayen guda 7 da suka hada da tsohon shugaban kasar Ecuador Rosalia Arteaga ba wata kasar da ta gabatar dasu a matsayan 'yan takara kawo yanzu.

Guterres, wanda ya kasance Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya tun a shekarar 2017, a matsayin dan takara daya tilo a zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya amsa tambayoyin kasashe mambobin kungiyar tare da yin jawabai akan matakan da zai dauka anan gaba.

Tsohon firaiministan Portugal, Guterres, wanda a baya ya yi aiki a matsayin Babban Kwamishinan ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya na tsawon shekaru 10, ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi kan wannan mukami a wa’adi na biyu, zai zama“ mai shiga tsakani da gaskiya ”kuma zai kasance “ maginin gada” a matsayin sabbin sallon neman hanyoyin magance rikice-rikice a doron kasa.

Guterres, wanda har yanzu shi ne Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana daidaito tsakanin maza da mata da kuma yaki da canjin yanayi a matsayan wasu daga cikin abubuwan da ya sanya a gaba a wannan matsayin da yake gudanarwa tsawon shekaru 4 da rabi.Labarai masu alaka