Bakin haure 28 sun tsallake rijiya da baya

An sanar da nasarar kubutar da 'yan gudun hijran dake yukurin ratsawa zuwa Turai cikin kwalekwalen roba ta barauniyar hanya daga garin dikili dake yankin Izmir

1636483
Bakin haure 28 sun tsallake rijiya da baya

An sanar da nasarar kubutar da 'yan gudun hijran dake yukurin ratsawa zuwa Turai cikin kwalekwalen roba ta barauniyar hanya daga garin dikili dake yankin Izmir.

Jami'an tsaron ruwan Turkiyya sun bayyana cewa an nemi su kai dauki ga bakin hauren da jirgin robansu ya lalace a tsakiyar teku lamarin da ya sanya suke daf da nutsewa.

A agajin da jami'an tsaron suka kai sun yi nasarar kubutar da bakin hauren daga cikin teku har su 28.

Bayan an kammala binciken farko an mika su ga hukumar 'yan gudun hijiran dake yankin.

 Labarai masu alaka