'Yan ta'addar PKK sun kaiwa mayakan Peshmerga hari a Erbil

'Yan ta'addar a ware na PKK sun kai hari kan mayakan Peshmerga a yankin Kurdawan Iraki Mai Cin Gashin Kansa.

1635303
'Yan ta'addar PKK sun kaiwa mayakan Peshmerga hari a Erbil

'Yan ta'addar a ware na PKK sun kai hari kan mayakan Peshmerga a yankin Kurdawan Iraki Mai Cin Gashin Kansa.

Labaran da wata kafa dake Erbil ta fitar na cewa, 'yan ta'addar na PKK sun kaiwa Peshmerga hari a unguwar Sidekan ta gundumar Soran dake Erbil.

Kwamandan Pesherga Bahrem Arif Yasin ya fitar da sanarwa game da batun inda ya ce, 'yan ta'addar PKK sun kai hari cibiyar Peshmerga a Sidekan, ba a samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon harin.

A ranar 12 ga Maris wani bam da 'yan ta'addar PKK suka ajje a yankin Sidekan ya fashe a lokacin da motar mayakan Peshmerga ke wucewa. Sojan Peshmerga 1 ya mutu, wani 1 kuma ya jikkata.

 Labarai masu alaka