Isra'ila ta kashe wani yaro Bafalasdine

Sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai a garin Nablus da Yahudawa suka mamaye a Yammacin gabar Kogin Jordan, wani yaro Bafalasdine mai shekaru 16 ya yi Shahada.

1635094

Sanarwar da Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent ta Falasdin ta fitar ta ce, sojojin Isra'ila sun kai  hari unguwar Odala ta garin Nablus tare da kashe matashin Bafalasdine mai shekaru 16.

Kungiyar ta bayyana karbar gawar matashin.

Sanarwar ta ce, wani matashin da aka jikkata a arangamar da aka yi kuma na kwance a asibiti.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin ta tabbatar da an kashe matashin Bafalasdinen a unguwar Odala amma ba ta bayyana sunansa ba.

 Labarai masu alaka