An sake zaben Sevil Atasoy a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya

An zabi Farfesa Dakta Sevil Atasoy a matsayin mamba ta Hukumar Kula da Magunguna ta Majalisar Dinkin Duniya (UN) a karo na uku.

1626102
An sake zaben Sevil Atasoy a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya

An zabi Farfesa Dakta Sevil Atasoy a matsayin mamba ta Kwamtin Kula da Magunguna ta Majalisar Dinkin Duniya (UN) a karo na uku.

An sake zaben Sevil Atasoy a matsayin mamba ta kwamitin da ke Vienna don aiki daga shekarar 2022 zuwa 2027 a zabukan da aka gudanar a Zauren Majalisar Dinkin Duniya kan Tattalin Arziki da Zamantakewa.

Atasoy wacce ta fara aiki a Kwamitin Kula da Magunguna ta Majalisar Dinkin Duniya daga shekarar 2005 zuwa 2010, ita ce 'yar kasar Turkiyya na farko da ta zama shugabar hukumar.

Kwamitin yana da mambobi 13.Labarai masu alaka