An kafa tarihin kamuwa da Corona a Indiya

An kafa tarihin kamuwa da cutar Corona a Indiya inda a awanni 24 da suka gabata cutar ta kama sama da mutane dubu 314.

1626198
An kafa tarihin kamuwa da Corona a Indiya

An kafa tarihin kamuwa da cutar Corona a Indiya inda a awanni 24 da suka gabata cutar ta kama sama da mutane dubu 314.

Wannan adadi maffi yawa da aka taba samu a kasa guda daya a duniya tun bullar cutar zuwa yau.

Kwararru sun yi gargadin cewa, yadda asibitoci suka cika saboda karuwar kamuwa da cutar, akwai yiwuwar tsarin kula da lafiya na Indiya ya ruguje.

Tun daga 2 ga Afrilu zuwa yau Indiya ta zama kan gaba a duniya wajen yawan masu kamuwa da cutar Corona.Labarai masu alaka