An sake samu hatsarin jirgin kasa da ya yi sanadiyar rayuka 8 a Masar

A garin Kalyubiye kasar Masar kaucewar wani jirgin kasa daga layin dogo yayin sanadiyar rayukan fasinjoji 8 da kuma raunanan fiye da 100

1623565
An sake samu hatsarin jirgin kasa da ya yi sanadiyar rayuka 8 a Masar

A garin Kalyubiye kasar Masar kaucewar wani jirgin kasa daga layin dogo yayin sanadiyar rayukan fasinjoji 8 da kuma raunanan fiye da 100.

Kamar yadda Hukumar Kula da Jiragen Kasa a kasar Masar ta sanar jirgin kasa mai lamba 949 a yayinda yake kan hanyarsa daga Alkahira zuwa Mansura ya kauce daga layin dogo a daidai garin Kalyubiye lamarin da ya sanya ficewa wagon hudu.

Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu an samu rasuwar mutum 8 inda kuma fiye da 100 suka raunana.

Tuni dai ma'aikatar bayar da agajin gaggawa sun bayyana a yankin domin bayar da ceto.

A ranar 26 ga watam Maris ma an samu hatsarin jirgin kasa a kasar Masar lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutum 32 da raunanan wasu 66.

 Labarai masu alaka