An jikkata mutane 2 sakamakon hari da makamin roka a Iraki

Mutane 2 sun samu raunuka sakamakon hari da makamin roka da aka kai a Sansanin Soji na Balad da ke jihar Salahaddin din kasar Iraki.

1623624
An jikkata mutane 2 sakamakon hari da makamin roka a Iraki

Mutane 2 sun samu raunuka sakamakon hari da makamin roka da aka kai a Sansanin Soji na Balad da ke jihar Salahaddin din kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Iraki ya shaida cewa, an harba makaman roka 2 zuwa Sansanin Sojin Sama na Balad.

Mutane 2 sun samu raunuka sakamakon harin.

A labaran ba a bayyana ko sojoji ko fararen hula ne suka jikkata ba.

Dakarun Amurka da suka jagoranci kawancen kasashen duniya, sun mikawa sojojin Iraki Sansanin Sojin Sama na Balad.

Akwai ma'aikatan kamfanin tsaro na Amurka na Sallyport Global da ke aiki a sansanin.

 Labarai masu alaka