Limamin Babban Masallacin Juma’a ya koma makaranta

Limamin Babban Masallacin Hagia Sophia mai dinbin tarihi dake birnin Istanbul ya bayyana cewa zai ajiye limanci domin komawa yin hidima a  harkokin ilimi

1618901
Limamin Babban Masallacin Juma’a ya koma makaranta

Limamin Babban Masallacin Hagia Sophia mai dinbin tarihi dake birnin Istanbul ya bayyana cewa zai ajiye limanci domin komawa yin hidima a  harkokin ilimi.

Mehmet Boynukalin, wanda ya kasance limamin Masallacin Hagia Sophia mai shekaru 1,500 a birnin Istanbul ya nemi ya ajiye limancinsa kuma an amince masa.

Zai ci gaba da aiki a fannin ilimi a Jami’ar Kimiyyar  Marmara dake kasar Turkiyya.

Boynukalin ya kasance yana hidima a Masallacin tare da wasu mataimaka biyu tun daga watan Yuli na shekarar bara, a lokacin da aka mayar da Hagia Sophia Masallacin .Labarai masu alaka