An yankewa sojoji uku hukuncin kisa a Saudiyya

Kasar Saudiyya ta sanar da yankewa sojoji uku hukuncin kisa akan kamasu da laifin "cin amanar kasa"

1618696
An yankewa sojoji uku hukuncin kisa a Saudiyya

Kasar Saudiyya ta sanar da yankewa sojoji uku hukuncin kisa akan kamasu da laifin "cin amanar kasa."

Kamar yadda kanfanin dillacin labaran Saudiyya ta SPA ta sanar ma'aikatar tsaron kasar ta kawo karshen binciken da take yiwa akan wasu sojojin kasar Saudiyya uku da ake tuhuma da laifuka daban-daban.

An yankewa sojojin uku hukuncin kisa ne akan laifin "cin amanan kasa" ta hada baki da masu adawa da kasar daga kasashen ketare da kuma "sabawa dokar sojin kasar"

Sanarwar ta kara da cewa, za'a yankewa sojojin uku hukuncin kisan ne bayana sarkin kasar ya bayar da umarnin hakan wanda za'a yi a Barikin sojojin dake Kudanci.

Binciken ya nuna cewa sojojin sun "hada baki da makiyan kasar " amma ba'a bayyana ko su wanenen makiyan ba.

 Labarai masu alaka