An yi wa 'yan ta'addar Daesh babbar barna a Turkiyya

Turkiyya da ke ci gaba da yaki da 'yan ta'addar Daesh, ta yi wa kungiyar babbar barna a watan Maris din da ya gabata.

1612755
An yi wa 'yan ta'addar Daesh babbar barna a Turkiyya

Turkiyya da ke ci gaba da yaki da 'yan ta'addar Daesh, ta yi wa kungiyar babbar barna a watan Maris din da ya gabata.

Jami'an tsaron Turkiyya sun lalata shirin 'yan ta'addar na zubar da jini a Ankara, Istanbul da wasu garuruwan Turkiyya da dama.

A watan Maris din da ya gabata, a aiyukan da jami'an 'yan sanda, jandarma da masu tsaron iyakar Turkiyya suka gudanar, sun kama mambobin Daesh 164 da suka hada da 'yan kasashen waje, an kuma kwace makamai da dama daga hannunsu.

An gurfanar da 26 daga cikin wadanda aka kama a gaban kotu. An kori wasu daga cikinsu zuwa ksashensu, ana ci gaba da bincikar wasun su.Labarai masu alaka