Harin bam a Resulayn

Fararen hula biyu sun rasa rayukansu, wasu 7 sun samu raunuka sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a cikin wata mota a yankin Resulayn da ke arewacin Siriya.

1590878
Harin bam a Resulayn

Fararen hula biyu sun rasa rayukansu, wasu 7 sun samu raunuka sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a cikin wata mota a yankin Resulayn da ke arewacin Siriya.

Gundumar Resulayn na daura da gundumar Ceylanpinar din lardin Sanliurfa na Turkiyya, kuma an tayar da bam din a cikin motar da aka ajje a wata kasuwar sayar da kaji.

Fararen hula 2 sun rasa rayukansu, wasu 7 kuma sun jikkata sakamakon harin.

Jami'an tsaron da suka fara gudanar da abincike sun bayyana cewa, akwai yiwuwar 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suka kai harin.Labarai masu alaka