Firaministan Armeniya ya kori Babban Hafsan Hafsoshin kasar

Firaministan Armeniya, Nikol Pashinyan ya kori Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Onik Gasparyan wanda ya kira shi ya yi murabus.

1590586
Firaministan Armeniya ya kori Babban Hafsan Hafsoshin kasar

Firaministan Armeniya, Nikol Pashinyan ya kori Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Onik Gasparyan wanda ya kira shi ya yi murabus.

Babban Hafsan Hafsoshin Armeniya da dukkan manyan kwamandoji sun fitar da sanarwa suna kira ga Firaminista Pashinyan da ya yi murabus.

An bayyana a cikin sanarwar cewa gwamnatin Pashinyan ba ta da ikon yanke hukunci mai tsauri da isa.

Bayan wannan, Pashinyan ya bayyana kiran sojojin da ya yi murabus a matsayin "yunkurin juyin mulki" kuma ya gayyaci magoya bayansa da su fita kan tutuna.

Pashinyan ya kuma sanar da cewa ya kori Babban Hafsan Hafsoshi, Gasparyan.Labarai masu alaka