Firaministan Iraki yayi magana kan harin da aka kai Erbil

Firaministan Iraki, Mustafa al-Kazimi ya ce makasudin kai harin makami mai linzami kan filin tashi da saukar jiragen sama na Erbil shi ne haifar da rudani.

1584896

A cikin bayanan nasa yayin taron Majalisar Ministoci da ake gudanarwa a kowane mako, Kazimi ya kimanta harin na makami mai linzami da ya nufi filin tashi da saukar jiragen sama na Erbil a jiya.

Firaministan na Iraki ya ce, “Manufar aiyukan ta’addanci shi ne haifar da rudani. Lamarin ya afku ne a lokacin da gwamnati ke kokarin kawo karshen rikici a yankin da kasar.”

Kazimi ya kara da cewa sun ba da umarnin a gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tsakiya da Gwamnatin Yankin Kurdawan Iraki (KRG) don bayyana wadanda suka kai harin.Labarai masu alaka