Girka ta kara yankinta a Tekun Ionia

Majalisar Dokokin Girka ta amince da kudirin dokar da ke yin la’akari da karin yankunan kasar daga mil 6 zuwa mil 12 a Tekun Ionia.

1567878
Girka ta kara yankinta a Tekun Ionia

Majalisar Dokokin Girka ta amince da kudirin dokar da ke yin la’akari da karin yankunan kasar daga mil 6 zuwa mil 12 a Tekun Ionia.

An amince da kudirin ne sakamakon kada kuri'a a fili.

Firaminista Kiryakos Micotakis, a jawabin da ya yi kafin kada kuri’ar, ya bayar da hujjar cewa kasarsa na da ‘yancin fadada yankin ruwanta kuma ya yi ikirarin cewa sun dauki matakai kan wannan batun daidai da dokokin kasa da kasa da dokokin Majalisar Dinkin Duniya (UN) na teku.

Girka da Italiya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar keɓance iyaka na Yankin Tattalin Arziki (EEZ) a cikin Tekun Ionia a ranar 9 ga Agusta.Labarai masu alaka