Afirka ta Kudu ta yiwa jakadiyar Amurka fatan warkewa daga Covid-19

Jakadiyar Amurka a kasar Afirka ta Kudu Lana Marks ta y ifama da kwauyar cutar Korona a kasar Afirka ta Kudu

1565198
Afirka ta Kudu ta yiwa jakadiyar Amurka fatan warkewa daga Covid-19

Jakadiyar Amurka a kasar Afirka ta Kudu Lana Marks ta y ifama da kwauyar cutar Korona a kasar Afirka ta Kudu.

An dai sanar da ware jakadiyar a sashen kulawar gaggawa dake cikin wani asibiti inda ta kasance na tsawon makonni.

Kasar Afirka ta Kudun ta yiwa jakadiyyar fatan samun sauki cikin gaggawa a wata sanarwar da ministan lafiyar kasar Zweli Mkhize ya fitar,

“Muna masu fatan samun sauki cikin kankanen lokaci ga kuma ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya a yayinda kike warkewa daga Covid-19.

An dai samu Marks da Korona bayan gwajin da aka yi mata a watan jiya sanadiyar alamomin da take dasu na zazzabi, gajiya da ciwon makogoro.

 Labarai masu alaka