Dakarun Rasha sun yi yunkurin shiga yankin Idlib na arewacin Siriya

Dakarun Rasha na Musamman sun yi yunkurin shiga yankin kudancin Idlib da ke arewacin Siriya, inda Mayakan Kasa na Siriya su ke rike da iko.

1561590

Bayanan da aka samu daga majiyoyin Dakarun Kasa na Siriya na cewa, Dakarun Musamman na Rasha da tsakar daren Litinin din nan sun yi yunkurin shiga yankin Gab Ovasi na gundumar Hama da ke kudancin lardin Idlib.

Sakamakon arangamar da ta barke a kan iyakar Enwaki bayan karya yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha da Turkiyya suka sanya hannu a kai, Mayakan Kasa na Siriya sun yi asarar rayuka.

Mayakan Kasa na Siriya sun kai harin mayar da martani da bam da makaman roka kauyen Maarat Mukhas, a lokacin dakarun gwamnatin Siriya suka yi yunkurin shiga kauyen.Labarai masu alaka