Amurka za ta tallafawa Sudan don biyan bashin Bankin Duniya

Gwamnatin Sudan ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da Ma’aikatar Baitul malin Amurka don ba ta sama da dala biliyan 1 duk shekara don biyan bashin da Bankin Duniya ke binta.

1558847

A cewar sanarwar da Ma'aikatar Kudi ta Sudan ta fitar an bayyana cewar Sakataren Baitul malin Amurka, Steven Mnuchin wanda ya je Khartoum, babban birnin kasar ya tattauna da Ministan Kudi na Sudan, Hibe Muhammed Ali a wani bangare na ziyarar aiki ta yini guda bayan shawarar da Amurka ta yanke na cire Sudan daga jerin jihohin da ke tallafawa ta'addanci.

Ministocin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Ma’aikatar Baitul malin Amurka kan bashin da Sudan ke bin Bankin Duniya, inda za su ba ta rancen sama da dala biliyan 1 a kowace shekara.

Ana sa ran Shugabar Bankin Fitar da Shigar da Kaya ta Amurka (EXIM), Kimberly Reed ita ma za ta ziyarci Khartoum gobe don tattauna batun dawo da Sudan kan tsarin Bankin Duniya.Labarai masu alaka