Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 63 a Japan

An sanar da cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rayukan mutane 63 a yankin Kyushu dake kudu maso yammacin kasar Japan

1453177
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 63 a Japan

An sanar da cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rayukan mutane 63 a yankin Kyushu dake kudu maso yammacin kasar Japan.

Ambaliyar ruwan ta haifar da cikowar ruwa a koguna 92 da rafin yankin Kyuşhu  da wasu yankunan jahohi goma.

Ambaliyar ruwan ya haifar da rushewar gidaje, faduwar bishiyoyi da rufewar tituna da kuma mamaye dubban gidaje.

A yankin Kyuşhu dake jihar Kumamoto yawan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar ruwan sun haura 63.

Haka kuma lamarin ya sanya an kwashe fiye da mutane miliyan 1.3 a yankin Kyuşhu.

 Labarai masu alaka