Japan zata sayi jiragen yaki daga Amurka

Amurka ta amince da siyarwa kasar Japan jiragen yaki 105 kirar F-35 akan kudi dala biliyan 23 a yayinda tashin hankali ke kara karuwa a yankunan tekun kudancin China tsakanin kawayen Amurka dana China dake yankin

1453269
Japan zata sayi jiragen yaki daga Amurka

Amurka ta amince da siyarwa kasar Japan jiragen yaki 105 kirar F-35 akan kudi dala biliyan 23 a yayinda tashin hankali ke kara karuwa a yankunan tekun kudancin China tsakanin kawayen Amurka dana China dake yankin.

Jiragen sun hada da na kirar F-35A guda 63 da kuma F-35 guda 42. Hakan ya biyo bayan matakin da Japan ta dauka na kara yawan makaman daga 42 zuwa 147.

Kasar Japan dai bata da wata babban manufa a yankin tekun kudancin China amma tana kallon yankin a matsayin hanya mai kwari domin shige da ficen kasuwanci.

 Labarai masu alaka