Mutane 28 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Bangaladash

Mutane akalla 28 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Bangaladash.

1445669
Mutane 28 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Bangaladash

Mutane akalla 28 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Bangaladash.

An bayyana cewar an ci gaba da aiyukan ceto bayan afkuwar hatsarin a kogin Buriganga da ke kusa da Dakka Babban Birnin Kasar.

Rozina Islam da ke aiki da Hukumar Kashe Gobara ta bayyana cewar karamin jirgin ruwan ya kife bayan yin karo da wani jirgin ruwan daukar kaya babba.

Kafafan yada labarai na kasar kuma sun ce akwai fasinjoji kusan 100 a cikin jirgin ruwan a lokacinda hatsarin ya afku.Labarai masu alaka