An kashe fararen hula 23 a Afganistan

Fararen hula 23 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai da makaman roka da kuma bam a wata kasuwa da ke Afganistan.

1445646
An kashe fararen hula 23 a Afganistan

Fararen hula 23 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai da makaman roka da kuma bam a wata kasuwa da ke Afganistan.

Fadar Gwamnan Helmand ta sanar da cewar an harba makaman roka 4 kan "Kasuwar Kuhne", daga baya kuma aka kutsa kai da mota dauke da bama-bamai kan dandazon jama'a.

Bayanan farko da aka samu sun ce fararen hula 23 ne suka mutu, wasu 15 kuma suka samu raunuka.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Kungiyar Taliban na rike da iko da mafiya yankunan gundumar Sangin ta jihar Helmand.Labarai masu alaka