'Rasha ta nemi baiwa Taliban cin hanci don ta kashe sojojin Amurka'

Fadar gwamtin White House ta sanar da cewa Rasha ta nemi ta baiwa kungiyar Taliban cin hanci domin ta kashe sojojin Amurka da kawayensu dake Afghanistan

1444742
'Rasha ta nemi baiwa Taliban cin hanci don ta kashe sojojin Amurka'

Fadar gwamtin White House ta sanar da cewa Rasha ta nemi ta baiwa kungiyar Taliban cin hanci domin ta kashe sojojin Amurka da kawayensu dake Afghanistan.

Shugaban kasar Amurka dai bai ce komai akan lamarin ba.

Mai magana da yawon fadar White House Kayleigh McEnany ta sanar da cewa an sanar da hukumar tsaron kasa da shugaba Trump akan yunkurin da Rasha ta yi na baiwa mambobin kungiyar Taliban kudade a asirce domin su kashe sojojin Amurka a watan Maris.

Jaridar New York Times ta rawaito cewa Rasha ta yi yunkurin baiwa kungiyar Taliban kudade a asirce domin ta kashe sojojin Amurka da kawayensu dake kasar Afghanistan.

Jami'an Amurka sun bayyana cewa an gano yunkurin baiwa Taliban cin hanci ne don su kashe sojojin Amurka a loacin da ake binciken wani mamaban kungiyar Taliban da aka kama.

 Labarai masu alaka