Ana ci gaba da la'antar Isra'ila bisa mamayar yankunan Falasdinawa da take yi

A Brussels Babban Birnin Kasar Beljiyom an gudanar da zanga-zangar la'antar yunkurin Isra'ila na gina sabbin matsugunan Yahudawa 'yan kama guri zauna a Yammacin Gabar Kogin da kuma mamaye Wadin Jordan da ta ce za ta yi.

1445052

Kungiyoyin farar hula da dama ne suka yi kira da a fita zanga-zanga a Brussels, inda dubunnan mutane suka taru a dandalin Trone da ke kusa da Ofishin Jakadancin Amurka.

Masu zanga-zangar sun dinga daga allunan da aka yi rubutun "Ki Yi tsawon Rai Falasdin", "Ku ce A'a ga mamayar kasar Falasdin", "Isra'ila na yin mulkin mallaka, Falasdin na shan wahala", "Jure Falasdin".

A yayin zanga-zangar an daga tutocin kasar Falasdin, yayinda a gefe guda kuma 'yan sanda suka dauki tsauraran matakan tsaro.Labarai masu alaka