MDD ta fara aiyukan yaki da yada bayanan karya game da Corona

Majalisar Dinkin Duniya ta fara wani yunkuri na kasa da kasa da nufin yaki da bayanan karya da ake fitarwa game da annobar Corona (Covid-19).

1421762

An ba wa yunkurin sunan "Verified" (Tabbatarwa) wanda a karkashin haka masanan kimiyya a yankunan duniya baki daya, daga bangarorin kafafan yada labarai, kungiyoyin fararen hula da kamfanoni masu zaman kansu za su dinga bayar da bayanai ta hannun 'yan sa kai.

Ta wannan kokari, Majalisar Dinkin Duniya za ta habaka tabbatar da yada bayanan gaskiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fitar da sakon bidiyo cewa "Ba za mu iya barin a ci gaba da yada karya, nuna tsana da shaci fadi a shafukan sadarwar zamani ba."

 Labarai masu alaka