An fafata kazamin rikici a Iran

'Yan sanda 2 sun rasa rayukansu a rikicin da suka fafata da 'yan bindiga a yankin kasar Iran da ke iyaka da Pakistan.

1421767
An fafata kazamin rikici a Iran

'Yan sanda 2 sun rasa rayukansu a rikicin da suka fafata da 'yan bindiga a yankin kasar Iran da ke iyaka da Pakistan.

Kamfanin dillancin labarai na Tesnim ya bayyana cewar da safiyar Juma'ar nan ne a gundumar Sebaz da ke jihar Sistan-Balujistan aka samu rikici tsakanin jami'an tsaro da 'Yan bindiga.

'Yan sanda 2 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar.

Ba a bayar da bayanan ko su waye 'yan bindigar ba a labaran da aka fitar.

Tag: #Rikici , #Iran

Labarai masu alaka