Yake-yaken soji a lokacin Corona

Duk da bulluwar annobar coronavirus, lamarin da ya kada zuciyar kasashe har ma da Amurka, rikice-rikicen gabas ta tsakiya na ci gaba da afkuwa ba kikkiftawa

1408953
Yake-yaken soji a lokacin Corona

Duk da bulluwar annobar coronavirus, lamarin da ya kada zuciyar kasashe har ma da Amurka, rikice-rikicen gabas ta tsakiya na ci gaba da afkuwa ba kikkiftawa. Majalisar Dinkin Duniya MDD ta yi kira da a tsagaita wuta a yankunan da ake rikici, amma a kasashen Libiya, Siriya da Yaman ana ci gaba da zubar da jini. Bugu da kari, a yayinda Lebanon ke ci gaba da fama da cin hanci da rashawa da matsalolin tattalin arziki, Iraki ta kasa magance matsalarta na dogaro akan man fetur. A wadanan kasashen, musanman Libiya, Siriya da Yaman  a maimakon yaki da corona suna daf ga afkawa cikin yakin basasa gaba daya. Babu daya daga cikin wadannan kasashen da za’a iya faiyace ainihin yawan wadanda suka kamu da kwayar cutar Covid-19. A yankunan da ake fadace-fadace annobar corona ta cudanye da rikice-rikicen da ake tafkawa. Duk da wannan halin da ake ake ciki hukumomin kasa da kasa basu dauki wasu muhimman matakan da suka wuce yin garga

A wannan makon mun kasancetare da Dkt. Murat Yeşiltaş ne daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya..

A Siriya dai zamu iya bayyana cewa ana yaki da corona a akallan yankuna hudu. A yankin da gwamnatin kasar keda iko an sanar da cewa Corona ta kama mutane 45 ne kachal. A yankunan Idlib da Ramazan kuwa an ga yadda ziyartar masallatai da yin sallar tarawi ya karu kwarai da gaske tun da aka fara azumin watan Ramadana. Wannan baya nuna cewa annobar bata bayyana a yankin Idlib ba. Musanman yadda yankin Idlib ya kasance mai dinbin al’umma da sansanonin ‘yan gudun hijira da dama. Ana dai ganin yadda Turkiyya ke taimakawa wajen hana yaduwar annobar a yankunan da sojoji masu zaman kansu ke da iko. Haka kuma a yankunan da YPG-PYD ke da iko wadanda Amurka ke goyawa baya babu masu cutar da yawa. Wa ya sani ko yakin shekaru goma da ya ki ci ya ki cinyewa a Siriya, ya zama alhairin hana yaduwar kwayar cutar corona a kasar.

 

A yayinda corona ke ci gaba da addabar ko wani sako, a Siriya ana ci gaba da tafka rikici. A yankin da aka fi aikata haka a kasar shi ne yankin Idlib. Yankin Idlib dai bai kasance yankin da ake tafka riciki kawai ba ya kuma kasance yankin da annobar ka iya barkewa. Bayan yarjejeniyar Moscow da Turkiyya da Rasha suka ayyanar a yankuna arewacin titunan M4 da M5 an karfafa matakan sojin yankin. Duk da dai ana ganin cewa hakan ka iya samar da wata mafita a yankin, akwai bukatar Ankara ta sake daukar wasu matakai a yankin bayan corona. Musanman yadda ake ganin yadda kungiyar Hayat Tahrir al-Sham ke ci gaba da kalubalantar matakan Turkiyya a yankin. Kungiyar Hayat Tahrir al-Sham bata amince da yawan wasu ka’idojin da aka cimma matsaya akansu a yarjejeniyar Moscow ba, sabili da haka suke ci gaba da daukan matakan kalubalantarsu. A ‘yan kwanakin da suka gabata kungiyar ta kai hari akan sojojin Turkiyya lamarin da ya yi sanadiyar shahadar soja daya. Sabili da haka ko shakka babu bayan yakar corona Turkiyya zata dauki matakai kwarara akan kungiyar Hayat Tahrir al-Sham. Haka kuma sanadiyar hare-haren da gwamnatin kasar ke kaiwa kusan mutane miliyan daya ke daf ga neman mafaka a yankin arewacin Idlib. A yayinda gwamnatin kasar ke kai hare-hare ta sama, ba dabara bace ga al’umman Idlib su kasance a cikin gidajensu don kauracewa coronavirus.

 

A gefe guda kuma, sojojin SMO masu adawa da gwamnatin kasar wacce Turkiyya ke goyawa baya na ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addan PKK-YPG a yankunan da suke da iko. Musanman a yankin da aka kaddamar da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya wacce aka fi sani da yankunan Rasul ayn da Tel Abyad. Su kuwa kungiyar ta’addar YPG na ci gaba da kai hari akan farar hula da kuma gurbata tsarukan samar da lumanar yankin. A yankin Afrin kuma PKK-YPG na daukar wata sabuwar sallo. A ranar 28 ga watan Afirilu sun kai hari da motar bam lamarin da ya yi sanadiyar rayukan farar hula fiye da 50. A yayinda a yankin da Turkiyya ke kula dasu, ‘yan ta’adda na ci gaba da kai hare-hare, kungiyar PKK na ci gaba da gurbata zaman lafiyar arewacin Siriya. Haka kuma kungiyar DEASH ta ci gaba da kai hare-haren kin kari a wadannan yankunan a cikin ‘yan makonnin da suka gabata. Suna labewa a iyakokin Siriya da Iraki suna kai hare-haren kin kari. Wadanan hare haren dai ala kulli halin nada nasaba ga irin gudunmowar da Amurka ke baiwa kungiyar YPG.

Gwamnatin Siriya wacce ke kokarin yin rufa-rufar corona na fuskantar matsalolin tattalin arziki. Musanamn yadda farashin mai ya fada warwas a kasuwar duniya da kuma yadda takunkumai ka kalubalantar tattalin arzikin Rasha da Iran. Ko Siriya zata kasance cikin wata sifa bayan Corona? wannan ba abu ne da za’a iya bayyanawa nan take ba, amma ga dukkan alamu kasashe masu fada aji a yankin zasu dauki sabbin salo bayan magance Covid-19.

 

A kasar Libiya kuwa lamari ya munana. Duk da MDD ta yi kira da a tsagaita wuta a ranar 22 ga watan Maris domin karfafa yakar cutar Corona, Mayakan Hafter sunki amincewa da hakan inda suka zabi ci gaba da kai hare-hare. A yayinda gwamnatin Trablus ke kokarin kalubalantar kwayar cutar corona mayakan Hafter na kaiwa cibiyoyin harkokin kiwon lafiya da suka da asibitoci hari da ganga. Duk da haka halattaciyar gwamnatin Libiya bata baiwa mayakan Hafter da Hadaddiyar Daular Larabawa ke goyawa baya damar karbe ikon Trablus ba. Sabanin haka sun kori mayakan Hafter daga wasu muhimman gurare tare da haifar musu da hasarori. Duk da haka dai har ila yau suna rike da ikon yankunan kudancin Trablus. Jamar Hafter ganin bai samu yadda yake soba, a ranar 28 ga watan Afirilu ya kafa majalisa a tsakiyar Tobruk inda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar dukkan Libiya. Sai dai bayanan da suka fito daga Moscow na nuna cewa wannan matakin na Hafter ba zai haifar masa da wani da mai ido ba. Ministan harkokin wajen Rasha Lavrov, ya bayyana cewa wannnan ba mataki da Hafter ya kamata ya dauka ba ne. Su ma al’umman Benghazi basu amince da wannan matakin ba, kuma sun yi watsi dashi lamarin dake nuna cewa basu bukatar Ghadafi karo na biyu. A karshe dai Hafter bai samu yadda yake so ba kuma yana ci gaba da rasa karfinsa. Sai dai hakan baya nuna cewa za’a samu fara’a a Libiyar. Sabili da   ayayinda ake fama da annobar corona, faduwar farashin man fetur, rikicin datti, rikice-rikice da matsalar wutar lantarki na daf ga gurfanar da kasar ta Libiya. Hakan na kara sanya rashin mutunta kasar da al’umman Libiya basu yi, haka kuma kasancewar yadda hukumomin kasa da kasa suka kasa daukar wata ingantattar mataki na kara nuna cewa kasar zata kara fadawa cikin rikici.

Ita kuwa Yaman, kafin ma bulluwar annobar corona ta kasance daya daga cikin kasashen dake fama da masifu. Kawo yanzu dai kasancewa mutum daya aka bayyana dauke da cutar a kasar. Yaman ta kasance daya daga cikin kasashen da annobar bata yi wata tasiri ba. Kasancewar yadda Saudiyya ce ta fara daukar matakin hana yaduwar cutar a kasar Yaman ya sanya ganin dakatar da hare-haren soji a kasar, sai dai hakan baya nuna kawo karshen matakan soja da ake dauka a kasar baki daya.

Barkewar annobar corona dai bai dakatar da rikice-rikicen gabas ta tsakiya ba; amma ta yi nasarar canja akalar masifun.

Wannan sharhin Dkt. Murat Yeşiltaş ne daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya..Labarai masu alaka