Mummunar ambaliyar ruwa a Iran

Mutane 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a kudancin Iran.

1394520
Mummunar ambaliyar ruwa a Iran

Mutane 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a kudancin Iran.

Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa Mujtaba Halidi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na daliban Iran ISNA cewar "Daga ranar 22 ga Maris zuwa yau mutane 26 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a kasar."

Kakaki Halidi ya kuma cewa a awanni 24 da suka gabata wani mutum 1 ya mutu sakamakon ambaliyar ruwan a jihar Yezd, wani mutum 1 kuma ya bata.

Tun ranar 22 ga Maris ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a kudancin Iran wanda ke kuma janyo asarar ga kasar.Labarai masu alaka