Adadin wadanda coronavirus ta kashe ya haura na harin 11 ga Satumba a New York

An sanar da cewa sabuwar kwayar cutar coronavirus (Covid-19) ta salwantar da rayuka da yawa fiye da na harin ta'addancin 11 ga watan Satumba a birnin New York dake Amurka

1394423
Adadin wadanda coronavirus ta kashe ya haura na harin 11 ga Satumba a New York

An sanar da cewa sabuwar kwayar cutar coronavirus (Covid-19) ta salwantar da rayuka da yawa fiye da na harin ta'addancin 11 ga watan Satumba a birnin New York dake Amurka.

Walin New York Andrew Cuomo ya tunatar da cewa adadin mutanen da suka mutu sanadiyar sabuwar cutar coronavirus ya karu da 779 a cikin kwana daya zuwa dubu 6 da dari 268 a jumlace, lamarin da ya haura yawan mutanen da suka rasa rayukansu dubu 2 da dari 753 a harin ta'addancin da aka kai a ranar 11 ga watan Satumba a birnin na New York.

A ranar 11 ga watan Saumban shekarar 2001 ne wasu mambobin Al-Ka'ida 'yan ta'adda suka kwace wasu jiragen sama hudu bayan sun tashi a Amurka.

Jiragen biyu sun doki tagwayen ginar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya dake birnin New York lamarin da ya haifar da rushewar tagwayen ginan masu hawa 110.

Jirgi na uku ya doki sashen yamman ginan ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon dake jihar Virginia lamarin da ya sanya rushewar sashen ginan.

Jirgi na hudu kuwa ya tunkari babban birnin kasar watau Washington amma sakamakon kalubalantar 'yan ta'addan da fasinjoji suka yi jirgin ya fadi a yankin Pennsylvania.

 Labarai masu alaka