Daraktan WHO ya bukaci jama'a su yi amfani da lokacinsu wajen yaki da Corona

Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fadawa jama'ar kasashen da aka hana fita waje a cikinsu da su yi kyakkyawan amfani da lokacin wajen yaki da cutar Corona (Covid19).

1385338

A wajen taron manema labarai ta hanyar Telekonferans da aka gudanar a helkwatar WHO dake Geneva ya ce "A baya mun samu nasarar yaki da annoba da rikici iri-iri. Wannan ma za mu yi nasara a kanta. Tambayar dai ita ce wacce irin asara za mu yi?.

Ya ce "Umartar mutane da su zauna a gidajensu na hana yawaitar zirga-zirgar jama'a, hakan na samar da lokaci sannan yana rage wahalar da sashen kula da lafiya."

Ya kuma kara da cewar wannan mataki kadai ba zai kawar da annobar ta Corona (Covid-19) ba.

Ghebreyesus ya yi kira ga dukkan jama'ar dake kasashen da aka hana fita da saboda Corona da su yi amfani da lokutansu wajen yakar annobar.

Ya ci gaba da cewa "Wannan mataki shi ne zai hana yaduwar cutar tare da dakatar da ita. Hakan ne hanya mafi kyau da dacewa. Idan aka ci gaba da haka har lokacinda aka sanar da janye matakan to ba za a sake ganin cutar ba.

Ghebreyesus ya yi gargadi da cewar kafin a sake bude makarantuda wuraren aiyuka sai an kammala yaki da cutar gaba daya, idan ba haka ba to annobar za ta sake barkewa sosai.

Daraktan na WHO ya ce hanya mafi kyau da sauri kuma cikin saukin kashe kudi wajen magance cutar ita ce, kebe kai, yin gwaji, gano cutar da fara yi mata magani nan da nan.Labarai masu alaka