Mutuwar wani sanadiyar sabuwar cutar Hantavirus ya kara tada hankalin al'umman China

Mutuwar wani mutum da ya kamu da sabuwar cutar Hantavirus da ake dauka daga beraye a kasar China da coronavirus ta bulla ta sake tayar da hankalin al'umman kasar

1384267
Mutuwar wani sanadiyar sabuwar cutar Hantavirus ya kara tada hankalin al'umman China

Mutuwar wani mutum da ya kamu da sabuwar cutar Hantavirus da ake dauka daga beraye a kasar China da coronavirus ta bulla ta sake tayar da hankalin al'umman kasar.

Dangane ga kafar yada labaran kasar China mai suna Global Times, a jihar Yunnan dake yammacin kasar inda aka bayyana bulluwar Hantavirus wani mutum ya rasa ransa bayan kamuwa da cutar a yayinda yake kan hanyarsa cikin bas zuwa jihar Shantung.

An tabbar da cewa an yi wa dukkanin fasinjojin dake cikin motar bas din gwaji.

Bayan labarin da Global Times ta fitar, labarin hantavirus ya yadu a kafafen sadar da zumunta inda aka rinka sharhi a karkashin maudu'i mai taken "hantavirus" a kafar Twitter.

Hantavirus wanda ake dauka daga beraye, kashinsu ko fitsarinsu na haifar da cutar huhu da ake kira "Hantavirus Lung Syndrome" (HPS), an tabbatar da cewa baya yaduwa daga mutum zuwa mutum sabili da haka babu hadari game da yaduwarsa.

 Labarai masu alaka