Corona: Gubar sinadaran wanke hannu ta yi ajalin mutane 3 a Iran

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon shakar warin abubuwan wanke hannu da suka ajje a dakunan da suke a rufe.

1384602
Corona: Gubar sinadaran wanke hannu ta yi ajalin mutane 3 a Iran

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon shakar warin abubuwan wanke hannu da suka ajje a dakunan da suke a rufe.

Shugaban Jami'ar Kiwon Lafiya ta Shehrikurd Majid Shirani ya zanta da kamfanin dillancin labarai na ISNA.

Ya ce wasu mutane 3 a jihar Chaharmahal-Bahtiyar sun rasa rayukansu bayan amfani da hadin sinadaran wanke hannu a wajen da yake a rufe kuma babu iska a ciki.

Shira ni ya ce akwai damuwa sosai game da yadda abubuwan wanke hannu suke cutar da huhun dan adam a Iran.

A Iran an bayyana cewar sama da mutane dubu 1 ne suka kamud a rashin lafiya yayinda 219 daga ciki suka mutu sakamakon shan giya mara ingance bayan samun lamarin tana bayar da kariya daga cutar Corona (Covid-19).

 Labarai masu alaka