Annobar Corona a gabashin duniya

A dai-dai lokacinda cutar Corona (Covid-19) ke ci gaba da yaduwa, gabashin duniya na samun asarar rayuka daga cutar.

1384865
Annobar Corona a gabashin duniya

A dai-dai lokacinda cutar Corona (Covid-19) ke ci gaba da yaduwa, gabashin duniya na samun asarar rayuka daga cutar.

A Iran da sama da mutane dubu 2 suka mutu, duniya ta girga bsa yadda wani yaro dan shekaru 6 ya mutu. Daga cikin wadanda suka mutu har da wani Shugaban 'yan sanda.

A Iran mutane 4 sun sake mutuwa wand aya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutum 27, jimillar mutane 316ne suka kamu da cutar a kasar. Wasu 75 kuma sun warke.

A yankin Zirin Gaza da ya zuwa yanzu aka samu mutum 1 dauke da cutar, Hukumar Kula da Kungiyoyi da Harkokin Addini ta sanar da cewar a karkashin yaki da annobar cutar Corona (Covid-19) an dauki matakin rufe dukkan Masallatan yankin har nan da makonni 2.

Kakakin Ma'aikatar Lafiya dake Zirina Gaza Ashraf Al-Kudra ya bayyana cewar sakamakon rufe hanyoyin yankin da Isra'ila ta yi na tsawon shekaru 13 ya sanya babu isassshun kayan aiki a dakunan binciken lafiya, sannan ana da nakasun kaso 39 na magungunan dole, kaso 23 na kayan aiki da kaso 60 na jini da ake bukata. Kudra ya ce Isra'ila ce ke da alhakin rayuwar Falasdinawa, kuma matsin lamba da hana kai kayan kula da lafiya zuwa yankin Zirin Gaza da Isra'ila ta yi ya jefa rayuwar Falasdinawa cikin hadarin kamuwa da Corona (Covid-19).

Kudra ya sake yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta yi duk mai yiwuwa waje ganin an janye mamaya da rufe hanyoyin Zirin gaza da aka yi sannan ta aike da kayan kula da lafiya da suka hada da injinan numfashi, magunguna, kayan aiki da na dakunan bincike.

A Isra'ila kuma mutane 3 ne suka rasa rayukansu daga cikin 930 da suka kamu da cutar ta Corona (Covid-19). An sake samun karin mutane 274 da suka kamu.

An bayyana cewar a sansanin NATO dake Afganistan an samu sojojin kasashen waje 4 dauke da cutar Corona (Covid-19). Ana fadin cewar sojojin 'yan kasar Italiya ne.

 

Gwamnatin Masar kuma ta bayyana cewar mutane 19 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, wadanda suka kamu da ita kuma sun kai mutane 366 kuma ta sanar da hana fita waje tsakanin karfe 19.00 zuwa 06.00.

 

A Morokko mutane 170 cutar Corona ta kama inda 5 daga ciki suka rasa rayukansu.

A kokarin da Indiya ta ke na hana cutar Corona (Covid-19) yaduwa an hana jama'ar kasar fita waje na tsawon kwanaki 21.

Najeriya kuma da take nata kokarin hana yaduwar cutar ta rufe dukkan iyakokinta na kasa na tsawon makonni 4, Ivory Coast kuma ta sanar da dokar hana fita daga ranar Talatr nan daga karfe 21.00 zuwa 05.00.Labarai masu alaka